(ABNA24.com) A jiya Litinin ne dai kotun daukaka karar ta soja a jahar Bulaidha ta kasar Aljeriya, ta yanke hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 15 ga Sa’id Butafliqah wanda dan’uwan tsohon shugaban kasar ne, Abdulaziz Butafliqa.
Bugu da kari, kotun daukaka karar ta soja ta daure Bashir Dardaq, wanda shi ma tsohon jami’in gwamnatin Abdulaziz Butafliqa ne.
An sami mutanen ne dai da laifi kitsawa daular Aljeriya makirci.
/129